Sayyid Nasrallah da Nakhaleh sun yi nazari kan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a yankunan zirin Gaza da yammacin kogin Jordan, tare da yin dubi a kan yakin da aka yi da Isra'ila ta kaddamar kan yankunan Falastinawa a kwanakin baya-bayan nan.
Sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi fagage na siyasa a bangarori daban-daban na yankin, da kuma rawar da ake sa ran bangarorin daban-daban za su taka a fagen gwagwarmaya a mataki na gaba wajen tunkarar zalunci da mamayar Isra’ila a Falastinu, da kuma ayyukanta na tsokana da wuce gona da iri a kan wasu kasashen larabawa na yankin.